Kasar Amurka na kokarin hana rikici tsakanin Isra’ila da kungiyar Hizbullah

0 212

Amurka na aiki don hana wani babban rikici tsakanin Isra’ila da kungiyar Hizbullah ta Lebanon, bayan da aka kara kai ruwa rana tsakanin abokan gaba a kan iyakar kudancin Lebanon, a cewar wakilin Amurka, Amos Hochstein, Ajiya  Talata.

Tsawon watanni 8 da suka gabata kungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran da Isra’ila suna ta musayar wuta.

A baya-bayan nan kungiyar Hizbullah ta kai hare-haren rokoki da jirage marasa matuka a sansanin sojin Isra’ila bayan harin da Isra’ila ta kai ta kashe babban kwamandanta.

Da sanyin safiyar jiya Talata, Hochstein, mai magan da yawun  Joe Biden na Amurka, ya gana da shugaban sojojin kasar Lebanon.

Kasashen Amurka da Faransa duka suna yin kokarin diflomasiyya don cimma yarjejeniyar kawo karshen tashin hankalin da ke kan iyakar Lebanon. 

Kungiyar Hizbullah ta ce ba za ta dakatar da kai hare-hare ba matukar ba a tsagaita bude wuta a zirin Gaza ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: