Kasafin kudin shekarar 2024 zai bada damar kawar da fatara a kasar nan

0 263

Ministan bada agaji da yaki da talauci Beta Edu, tace kunshin kasafin kudin shekarar 2024 da aka warewa ma’aikatar ta zai bada damar kawar da fatara a kasar nan.

Ministan ta fadi haka ne yayin da ta bayyana a gaban Majalisar dokokin kasar nan domin kare kasafin kudin ma’aikatar bada agaji da yaki da talauci.

Tace an warewa ma’aikatar ta Naira Bilyan 532.2 wato kaso 28 daga cikin kasafin kudin shekarar 2024, domin rage radadin tsadar rayuwa da ake fama da shi a kasar nan.

Beta Edu, tace ma’aikatar nada shirye-shirye masu tarin yawa da take muradin cimma su.

Kazalika, ta kara da cewa Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da kirkirar asusun yaki da talauci na ma’aikatar bada agaji.

A cewar ta,ana sa ran asusun zai samu tallafi daga gwamnatin tarayya, da kuma kaso 30 daga hukumomin bada agaji,kasashe da sauran kungiyoyin cigaba.

Ministar ta bukaci kwamitin kula da kasafin kudi na majalisar da ya tallafawa ma’akatar domin gudanar da ayyukan ta. Shugaban kwamitin a Majalisar Dattawa Sanata Idiat Adebule, yayi alkawarin cewa kwamitin zai duba na tsanaki kan kasafin kudin ma’aikatar bada agaji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: