Karar Kwana: Yan Mata 9 Sun Sheka Lahira A Hatsarin Kwale-kwale A Zaria

0 260

Yan mata 9 sun gamu da ajalinsu yayin da suke kokarin tsallaka kudiddifin Galma dake yankin Tudun Wucicciri a garin Zaria na jihar Kaduna.

Wasu daga cikin wadanda suka iya tsallake rijiya da baya Fatima Idris da Faiza Abdullahi sun shaidawa cewa, hatsarin ya faru ne ranar Juma’a da karfe 12:00pm a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga Hayin Sarkin Fito bayan da aka gama sheka ruwa kamar da bakin kwarya.

Suka ce “Mu 16 ne a cikin jirgin amma yayin da suka kusan isa gab da gaba kawai sai ya fara nitsewa.”

Da yake jawabi kan batun, Mai unguwar Tudun Iya Alhaji Muhammadu Musa, ya bayyana cewa wannan shi ne babban iftila’i mafi girma da ya taba faruwa a yankin nasa.

Malam Musa ya kuma shaida cewa, a ranar da lamarin ya afku sun samu damar lalubo gawar biyar daga ciki yayinda washegari kuma suka fiddo da gawar karin wasu uku a kauyen Kaku sannan kuma suka sake tsamo gawar karshe a kauyen Garu Rubuchi kusan tazarar Kilo Mita 5km daga ainihin inda hatsarin ya faru.

Kana ya kuma kara da cewa dukkannin gawarwakin an binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Daga karshe ne kuma yayi jan kunne ga duk masu amfani da kwale-kwalen wajen hanyar sufuri da su rinka sanya lafiya a farko kafin komai, su kuma gujewa sanya mutane da yawa don samun kudi.

Shi dai wannan Kudiddifi na Galma da jirgin ruwan ya kife a cikinsa yana sadar da garin ne zuwa Kudiddifin Kubau dake karamar hukumar Kubau a Kaduna.

Yayin ziyarar gaisuwa da ta’aziyyar da ya kai yankin, dan majalisa jiha mai wakiltar Zaria Suleiman Wakili ya bayar da gudunmawar sabbin Kwale-kwale biyu ga al’ummar yankin domin saukaka zirga-zirga a garin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: