Karanta don sanin inda aka kwana a taƙaddamar ASUU da Gwamnati

0 343

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta bayyana umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da albashin wadanda basu shiga sabon tsarinta na hadakar biyan albashi da tattara bayanai IPPIS, a matsayin wata hanyar nakasasu domin tilasta musu shiga tsarin.

Shugaban kungiyar reshen jami’ar fatakwal Dr. Austen Sado, yace ko da yake wasu cikin abokan aikinsa, basu sami albashinsu ba tun watan fabarairun da ya gabata, said ai hakan, ba zai sanya kungiyar yin na’am da tsarin ba. Da ake hira dashi ta wayar talho, Sado yace umarnin na gwamnatin tarayya dangane da dakatar da albashinsu, manuniya ne cewa, akwai wani abu da take boyewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: