Majalisar Karamar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa ta sayi bandir din yadudduka 100 domin rabawa marayu 600 domin bikin Sallah mai zuwa.
Wannan shiri, a cewar shugaban karamar hakumar, Farfesa Abdurrahman Lawan, na da nufin baiwa wadanda suka ci gajiyar damar gudanar da bukukuwan cikin farin ciki.
Farfesa Lawan, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin na jihar Jigawa, ya bayyana hakan a jiya Lahadi, jim kadan bayan wata ganawa da sarakunan gargajiya a yankin.
A cewar Farfesa Abdulrahman Lawan, an zabo marayu 100 daga kowace gunduma da ke yankin domin raba musu kayyakin.
Ya kara da cewa majalisar ta ware naira dubu 600 domin biyan kudin dinki.
Shugaban ya jaddada kudirin majalisar na tallafawa marayu.
Lawan ya jaddada cewa wannan shiri na daya daga cikin kokarin majalisar na ganin marayun sun yi bukukuwan Sallah da ba za a manta da su ba kamar sauran su.