Shugaban karamar Hukumar, Malam Zaharadeen Abubakar ya sanar da haka lokacin taron kwamitin tsaro da na masu ruwa da tsaki
Ya ce karamar Hukumar ta umarci jami’an tsaro dasu kama tare da daukar matakan da suka dace ga duk wanda ya saba wannan umarni
Mallam Zaharadeen Abubakar ya kuma nuna takaicinsa ga masu yin halin ko in kula akan haramta noman kan Dutsi a Mana da Wosu da Laya da Lela kwayi da Dan Gulan dama sauran sassa
Ya kara da cewar karamar Hukumar ba za tayi kasa a gwiwa ba na hukunta masu aikata hakan