Karamar Hukumar Guri ta bayar da kwangilar sanya fitilun kan titi masu amfani da hasken rana a garin Wareri kan kudi naira miliyan 17
Karamar Hukumar Guri ta bayar da kwangilar sanya fitilun kan titi masu amfani da hasken rana a garin Wareri kan kudi naira miliyan 17.
Shugaban karamar hukumar Guri, Musa Shuaibu Muhammad Guri, ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse.
Musa Shuaibu ya kara da cewar Karamar Hukumar ta kuma bayar da kwangilar gina dakin haihuwa a garin Adiyani kan kudi naira miliyan 11 domin tallafawa mata masu juna biyu a yankin.
Yace suna fatan kammala ayyukan akan lokaci kasancewar an bayar da aiyukan ga manyan kamfanoni.
Shuganan karamar ya kara da cewar a watan da ya gabata Karamar Hukumar ta bayar da kwangilar tona fanfunan tuka-tuka guda biyar daga kudaden harajin karamar hukumar.