Karamar Hukumar Gumel ta jaddada kudirinta na kare lafiyar al’ummar yankin

0 221

Mukaddashin shugaban karamar Hukumar Alhaji Haladu Musa Mele ya bayyana hakan a lokacin taron tattaunawa da jamian hukumar tsaftar mahalli ta jiha da kungiyoyi da masu gidajen sayarda biredi da masu gidajen sayar da abinchi da kuma masu gidan ruwa na pure water.

Yace aikin kwashe shara da hukumar take gudanarwa, ya sake baiwa karamar hukumar kwarin gwiwa wajen gudanar da aikin tsaftar mahalli.

A nasa jawabinsa mukaddashin manajan daraktan hukumar tsaftar mahalli ta jiha ,  Adamu Sabo yace sun ziyarci yankin ne domin gudanar da aikin tsaftar mahalli da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan tsaftar mahalli.

Ya kuma bukaci yan kungiyoyi dasu yi koyi da karamar hukumar Gumel wajen gudanar da aikin tsaftar mahalli A jawabansu daban daban shugaban gidauniyar masarautar Gumel Malam Usman Suleiman da shugaban kungiyar sadarwa ta GUBLE Media Initiative and Empowerment Forum Malam Abdulmajid sun bada tabbacin cigaba da mara baya wajen ganin an tsaftace garin Gumel baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: