An shawarci gwamnatin tarayya da ta sauya tsarin shekarun ritayar ma’aikata da kuma yin watsi da bukatun kungiyoyin kwadago na kasar nan.
Wata farfesa a fannin jagoranci da ba da shawara, a Jami’ar Ilọrin Mary Grace Fajonyomi ce ta bada wannan shawarar ga gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a cikin littafinta mai shafuka 55 a bikin lacca karo na 238 na bude jami’ar.
Ta yi nuni da cewa, kara yawan shekarun yin ritaya zai kara tabarbare matsalar rashin aikin yi ga dimbin matasan da suka kammala karatu, musamman wadanda suka fito daga manyan makarantu.
Ta ce sabanin bukatar ma’aikata a kan lamarin, gaskiyar magana ita ce Najeriya na bukatar rage shekarun ritayar manyan ma’aikata domin magance rashin aikin yi.
Ya ce hakan ba zai haifar da takaici kadai ba, har ma da sauran matsalolin zamantakewa dake addabar matasa a kasar nan.