Kano Pillars ta karbe jagorancin gasar Firimiyar Najeriya

0 373

Kano Pillars ta dare saman teburin gasar Firimiyar Najeriya da maki 30, bayan samun nasarar doke Kwara United da kwallaye 2-0 a ranar Laraba.

Yayin fafatawar ta jiya ‘yan wasan Pillars Usman Babalolo da Rabi’u Ali ne jefa kwallayen 2 a ragar Kwara United.

Kafin tayi tattaki zuwa wasan da ta sha kaye a Kano, Kwara United ce ke jagorantar gasar Fimiyar Najeriyar ta bana da maki 27 bayan wasanni 15.

Sakamakon wasan da Enugu Rangers za ta fafata da Katsina United ne zai fayyace ko Pillars za ta cigaba da zama jagorar Firimiyar ko kuma za ta koma mataki na 2.

Leave a Reply

%d bloggers like this: