Kano Pillars na shirin daukar dan wasan Kamaru daga Morocco

0 253

Wani labari daga birnin Kano na nuni da cewa kungiyar Kano Pillars na shirin kammala yarjejeniyar daukar wani dan wasa dan asalin kasar Kamaru domin takawa kungiyar wasa a kaka mai kamawa.

Dan wasan mai suna Ngweni Ndasi ya kasance yana taka ledarsa ne a kungiyar CRA de Morocco, dake kasar Moroccan.

Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan ya iso jihar Kano ne tun a ranar Laraba kuma har ya kammala gwajin tabbatar da lafiyarsa a babban asibitin koyarwa na Abdullahi Wase Specialists Hospital, Kano, a yau Alhamis, har ma yayi atisayen farko da kungiyar a karamin filin wasa ga Dawakin Kudu.

Shugaban kungiyar Alhaji Surajo Shuaibu Yahaya, ya bayyana cewar ana kyautata zaton dan wasan zai rattaba kwantiragi da kungiyar a karshen makon nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: