Kamfanin Twitter ya sake goge sakon Shugaba Buhari

0 166

A wani labarin kuma, kamfanin Twitter ya goge daya daga cikin jerin sakonnin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa a ranar Talata.

Twitter ya goge inda shugaban ya ce matasan yanzu ba su san girman barna da hasarar rayukan da aka yi ba a yakin basasa ba. Mu da muka shafe wata 30 a fagen daga, muka ga bala’in yakin, za mu bi da su da salon da suka fi ganewa.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a yayin da yake ganawa da shugaban Hukumar Zabe ta ƙasa mai zaman kanta ta kasa INEC ranar Talata a fadarsa da ke Abuja.

Daga baya ne kuma Twitter ya goge sakon daga shafin shugaban na Najeriya.

Kamfanin na Twitter yace sakon ya sabawa sharuddansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: