Kamfanin Simintin BUA Ya Shirya Gogayya Da Simintin Dangote

0 361

Kamfanin simitin BUA, daya daga cikin manyan kamfanonin siminti a Afirka ta Yamma, ya shirya assasa wani katafaren kamfanin simiti da kamfanin samar da wutar lantarki a kananan hukumomin Guyuk da Lamurde na jihar Adamawa.

An sanar da haka lokacin da shugaban kamfanin BUA, Abdul-Samad Rabi’u, ya jagoranci tawagar manajojin kamfanin zuwa wata ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a gidan gwamnati dake Yola Babban birnin jihar.

Abdul-Samad Rabi’u yace binciken farko ya nuna cewa kananan hukumomin biyu suna da arzikin limestone mai inganci, kuma kamfanin BUA a shirye yake ya zuba jari a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: