Kamfanin NNPC ya musanta cewar ya soke yarjejeniyar kasuwanci da kamfanin Ɗangote

0 76

Kamfanin man NNPC ya musanta cewar ya soke yarjejeniyar kasuwanci da kamfanin Ɗangote domin sayar masa da gurɓataccen mai a farashin naira.

Mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye ya bayyana cewar, yarjejeniyar da suka ƙulla da Ɗangote domin sayar masa da man na watanni 6 ne, kuma za ta ƙare ne a ƙarshen wannan wata na Maris.

Soneye ya ce yanzu haka suna ci gaba da tattaunawa da kamfanin domin tsawaita yarjejeniyar.

NNPC ya ce tun bayan fara aikin matatar Ɗangote a shekarar 2023, an samar masa da ɗanyen mai ganga miliyan 84 a cikin gida, saboda haka ya yi watsi da zargin cewar ya soke yarjejeniyar ba shi man.

Leave a Reply