Kamfanin NNPC ya fara lodin mai ga manyan motoci a dukkan gidajen man fetur domin kawar da karancin man da ake fama da shi a Najeriya

0 193

A halin da ake ciki, kamfanin man fetur na kasa, NNPC, ya fara lodin mai ga manyan motoci a dukkan gidajen man fetur domin kawar da karancin man da ake fama da shi a fadin kasarnan.

Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin na NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja jim kadan bayan wani taro da kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa da direbobin tankar mai.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da kungiyar dillalan man fetur ta kasa da kungiyar manyan dillalan mai ta kasa.

Mele Kyari ya kara d a cewa akwai isasshen mai lita biliyan 1 da miliyan 700 na man fetur a halin yanzu.

Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin na NNPC ya ce Gwamnatin Tarayya da Hukumar Kamfanin NNPC ba su da wani shiri na kara farashin man fetur.

Ya kuma bukaci ‘yan kasuwa da su tabbatar sun sayar da man fetur a kan farashin da gwamnati ta amince da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: