Kamfani NNPCL ya musanta zargin rashin aukin man fetur ɗin da yake sayarwa

0 80

Babban kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya yi watsi da iƙirarin da wani mutum ya yi cewa man da kamfanin ke sayarwa bai kai na Dangote auki ba.

Cikin wani bidiyo da ya karaɗa shafukan sada zumunta an ga wani mutum da ya ce ya sayi man fetru daga kamfanin NNPCL a kan farashin naira 945, sannan ya sayi wani man a wani gidan mai da ke sauke man Dangote, a kan naira 925.

A cikin bidiyon mutumin ya yi iƙirarin cewa man Dangote ya zarta na kamfanin NNPLC daɗewa ana amfani da shi, inda har ya yi iƙirarin gwada mayukan biyu a injuna biyu, daga ƙarshe ya ce na NNPCL ya riga na Dangote ƙarewa da minituna fiye da 10.

To sai dai cikin wata sanarwar martani da NNPCL ɗin ya fitar ya ce gwajin da mutumin ya yi bai yi shi da ƙwarewa ba, sannan babu wata hujja ta kamawa a cikinsa.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa mafi yawan man da wannan gidan mai na NNPCL – da mutumin ya yi iƙirarin sayo man – daga kamfanin Dangote yake sayensa.

“NNPCL na jaddada ƙudirinsa na cewa man da yake sayarwa ana haɗa shi da ɗaya daga cikin manyan sidanarai masu inganci da ke taimakawa wajen tabbatar aukinsa da kuma rashin illa ga muhalli”, in ji sanarwar.

Daga ƙarshe ya gargaɗi masu irin wannan ɗabi’a cewa ba zai jure irin waɗannan ƙarairayi da ake shiryawa domin ɓata masa suna da kuma cutar da ƴan Najeriya ba.

Leave a Reply