Kalaman Shugaba Buhari Kan Kungiyar Kwadago Bisa Cikarta Shekaru 100

0 231

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya nanata jajircewar gwamnatinsa wajen samar da ayyuka ga dumbin matasan Najeriya.

Shugaban ya bayyana hakane yayinda yake zantawa da Darakta-Janar na Kungiyar Kwadago ta Kasa da Kasa, Mista Guy Rynder, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaba Buhari yace cikin shekaru 4, gwamnatinsa ta bayar da fifiko ga noma, da gidaje da kuma cigaban gine-gine.

Shugaba Buhari ya kuma gayawa shugaban kungiyar kwadagon cewa gwamantinsa ta tunkari matsalar karancin tituna, gadoji, digar jirgin kasa da kuma gidaje, gadan-gadan, domin tabbatar da yalwarsu zuwa shekaru dayawa masu zuwa.

Daga nan sai ya danganta nasarorin gwamnatinsa zuwa yanzu, da daukar shawarwari da tuntuba kafin yake duk wata babbar shawara da zata shafi ayyukan yi.

Shugaba Buhari sai yayi amfani da wannan damar wajen taya murna ga kungiyar kwadagon ta kasa da kasa bisa cikarta shekaru 100 da kafuwa.

Tunda farko, Mista Guy Ryder, ya shaidawa shugaban kasar cewa yazo Najeriya ne domin halartar taron samar da ayyuka ga matasa na duniya, inda kasashe sama da 60 suka hallara domin tattauna babbar matsalar samawa matasa aikin yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: