Gidauniyar yaki da kwararowar hamada da habbaka harkokin noma, ta samar da birtsatse mai anfani da hasken rana ga mutanen Shakato dake karamar hukumar Kafin Hausa.
Shugaban gudanarwa da tsare tsare na kasa, Thomos Famesor wanda yasi izinin mika fanfan burtsatsen ga al,ummar garin yace wannan aikin yana daya daga cikin aiyukan wannan kungiya ta samarwa mutanen kauyuka ingattaccen ruwa sha a jihar Jigawa.
Ya bayyana cewe tunda aka kirkiri Jahar aka dauki matakan yaki da kwararowar hamada da bunkasa harkokin noma tare da karfafawa matasa.
Yayin da yake jawabi mai wakiltar gidauniyar habbaka noma da samar da abinci ta kasa yace gidauniyar tana duba yadda za,a inganta ya banya a yan kunanna da suke hamada akasar.
A nasa bangaren shugaban karamar hukumar, Alhaji Garba Abdullahi yayi jawabin godiya ga gidauniyar a kokarinta na samar da rijiyar birtsatse mai anfani da haske rana a kauyen shakato, daga bisani yayi kira ga wanda suka anfana da birtsatsen da su yi anfani da shi ta hanyar da yace.