Joe Biden ya yi fatali da duk kiraye-kirayen janye takararsa da yan jam’iyyar Democrats ke yi

0 170

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi fatali da duk kiraye-kirayen janye takararsa da wasu kusoshi na jam’iyyar Democrats ke yi masa tun bayan da aka rinƙa nuna shakku a kan lafiyarsa.

A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ƙarshen taron ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO, Joe Biden ya ce yana burin kammala aikin da ya fara a Amurka. 

Shugaban ya kuma kare kansa daga sukar da yake sha cewar yaƙin neman zaɓensa na tafiyar hawainiya saboda alamun rashin cikakkiyar lafiya da tsufa da yake nunawa, inda ya ce ba bu gudu ba ja da baya, sai ya sake tsayawa takara a zaɓe mai zuwa, domin shi ne ɗan takarar da ya fi kowa cancanta.

Ya kuma yi amfani da taron maneman labaran wajen bayyana cewar ba shi da dalilin yin magana da shugaban Rasha Vladimir Putin, amma ya sha alwashin ci gaba da goyon bayan Ukraine, yana mai cewa gwamnatinsa na samun ci gaba wajen cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a Zirin Gaza.

A yayin taron manema labaran dai, na ranar Alhamis, Biden ya ruɗe har ya kira Trump a matsayin Kamala Harris wadda ta kasance mataimakiyarsa, amma duk da haka bai fasa batun nasa na sake tsayawa takara a babban na watan Nuwamba mai zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: