Jirgin ruwa ya nutse dauke da masu Mauludi 200 a Jihar Neja

0 248

Jirgin ruwa dauke da mutane 200 da ya tashi a daren jiya Talata daga yankin Mundi zuwa Gbajebo don zuwa bikin Maulidi a karamar hukumar Mokwa a Jihar Neja, ya nutse a ruwa.

Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne lokacin da jirgin ya doki wani itace da ke ƙarƙashin ruwan da ya taso a Kogin Neja.

Habibu Abubakar Wushishi, Daraktan Harkokin Yada Labarai da Tsare-tsare a Ma’aikatar Harkokin Jin-Kai, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce hatsarin ya faru ne a jiya talata 1 ga watan Oktoba, 2024, da misalin karfe 8:30 na dare.

Ya bayyana cewa tuni aka fara aikin ceto mutanen da suka nutse a ruwan.

Ya zuwa yanzu dai ba a san musababbin aukuwar hatsarin ba, amma ma’aikatar na aiki tare da Ma’aikatar Sufuri, Hukumar Kiyaye Hadura ta Jihar Neja, da Hukumar Ruwa ta Kasa don gudanar da bincike.

Abdullahi Baba Arah, Babban Daraktan Hukumar Kula da Hadura ta Jihar Neja (NSEMA), ya bayyana cewa mazauna yankin sun ceto mutane 150 zuwa yanzu.

Jibrin Muregi, Shugaban karamar hukumar Mokwa, ya tabbatar da lamarin amma ya ce har yanzu ba a san adadin wadanda suka rasu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: