Ana wani gagarumin aikin ceto a gabas da gaɓar tekun gabashin Ingila bayan tankar mai mallakin Amurka ta yi taho-mu-gama da wani jirgin ruwa na dakon kaya na Portugal a tekun North Sea.
Wakilin BBC ya ce wata sanarwa ta ce ana shirya kai ɗaukin gaggawa bayan samun rahoton tankar mai da jirgin ruwan dakon kaya sun yi karo.
Jirgin ruwan da kuma tankar sun kama da wuta yayin da wani bakin hayaki ke tashi a sama.
Jirage masu saukar ungulu da jiragen ruwa na kashe gobara duk sun kewaye wurin lamarin ya auku.