Jiragen Yaƙin Sojin Saman Najeriya sun yi wa sansanin ’yan ta’adda uku ruwan bama-bamai

0 179

Jiragen Yaƙin Sojin Saman Najeriya, sun yi wa sansanin ’yan ta’adda uku ruwan bama-bamai, inda suka hallaka da dama a Jihar Zamfara.

Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin sama, AVM Edward Gabkwet, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Gabkwet, ya ce rundunar Operation Hadarin Daji, sun lalata sansanin kasurguman ’yan bindiga da suka hada Abdullahi Nasanda da ke Zurmi, da Malam Tukur a Gusau, da kuma wasu a Karamar Hukumar Maradun.

Ya ce bayan samun bayanan sirri rundunar ta kai hari sansanin Nasanda, inda ’yan ta’adda ke boye makamai da babura. Yace Hare-haren da aka kai sun yi sanadiyyar mutuwar ’yan ta’adda da dama tare da ƙone kayayyakinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: