Kasa da jihohi 13 ne suka tsayar da ranar gudanar da zaben kananan hukumomi biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Alhamis din da ta gabata.
Kotun koli ta bayyana cewa ya sabawa kundin tsarin mulki gwamnonin jihohi su rike kudaden da ake warewa kananan hukumomi.
A hukuncin da mai shari’a Emmanuel Agim ya yanke, kwamitin mutum bakwai ya ce ya kamata kananan hukumomin kasar 774 su sarrafa kudaden su da kansu.
Kotun ta yanke hukuncin ne a cikin karar da Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) ya shigar a kan gwamnonin jihohi 36.
Kotun ta bayyana cewa gwamnonin jihohi 36 ba su da ikon rusa kananan hukumomin da aka zaba ta hanyar dimokradiyya domin maye gurbinsu da kwamitocin riko.