Kwamishiniyar Jin-kadai da Inganta Rayuwar Al’umma ta Jihar, Hajiya Hafsat Baba ta sanar da haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a birnin Kaduna, yayin da ta ce, jihar ta kuma karbi sama da Almajirai dubu 1 daga wasu jihohin daban.
Kwamishiniyar ta ce, wannan matakin da aka dauka, na cikin yunkurin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa, dukkanin kananan yara sun samu ilimin Al-Kur’ani da na zamani karkashin kulawar iyayensu.
Hajiya Hafsat ta ce, Ma’aikatarta tare da agajin Asusun Tallafa wa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNIECF, na kula da Almajiran da wasu jihohin suka taso keyarsu zuwa Kaduna.
- Obasanjo ba shugaban da za a yi koyi da shi bane – Gwamnatin Tarayya
- Aƙalla ‘yan ƙasar Nijar 300 ne ake zargin hukumomin Libiya sun tsare
- Mutum 7 sun mutu yayin zanga-zangar bayan zaɓe a Mozambique
- Da yiwuwar Amurka ta fitar da hannunta daga yaƙe-yaƙen ƙasashen ƙetare
- Ƙungiyar dillalan man fetur ta cimma matsaya da Dangote kan sayen man fetur
Gidan radiyon RFI ya rawaito cewa, Kwamishiniyar ta ce, wasu daga cikin Almajiran na fama da wasu nau’ukan cutuka da ke bukatar kulawa kafin sake sada su da dangoginsu.
Bullar abbobar coronavirus ce ta tilasta wa gwamnatocin johohin arewacin Najeriya mayar da dubban Almajirai jihohinsu na asali.