Jihar Jigawa zata zama jihar da tafi kowacce noman shinkafa a fadin Najeriya, a cewar gwamna Badaru

0 967

Gwamna Mohammed Badaru Abubakar yace bayan kaddamar da Filin Noma Kadada dubu 2,000 a Kazaure, da kuma Filin Noma Kadada dubu 6,000 a Madatsar ruwan rani a Hadejia da Auyo, nan bada jimawa ba jihar Jigawa zata zama Jihar data kowacce jiha Noman Shinkafa a fadin kasar nan.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin rangadin duba gonakin manoman shinkafa a kananun Hukumomin Auyo da Hadejia da kuma Jahun wadanda na daga daga cikin yankunan da gwamnatin tarayya ta ware kadadar noman rani dubu shida.

Yace yabanyar da ake samu ta shinkafa a yankunan abin alfahari ne wanda hakan ya sanya babu wata jiha da zata yi Gogayya da Jigawa wajen noman shinkafa.

Gwamna Badaru Abubakar yace jihar Jigawa karkashin shirin noma dan riba na Ma’aikatar aikin gona ya shigo da manoma da iyalansu cikin shirin yayinda aka tallafawa manoman da ingantaceen irin shuka da takin zamani da kuma maganin kwari.

Inda yace hakan na daga cikin kokarin gwamnatin Muhamamd Buhari na lalubo hanyoyin dogaro bunkasa tattalin arziki maimakon dogaro da man fetir da kuma fitar da miliyoyin yan Nigeria daga cikin kangin fatara da kuma talauci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: