Hukumar Shige da Fice ta Kasa reshen Jihar Jigawa ta kubutar da Mata 7 da akayi safarar su daga jihohi daban-daban na kasar nan.
Kwamandan Hukumar na Jihar Jigawa Isma’il Baba, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, inda ya ce sun kubutar da mutanen ne a kyauyen Gurai na karamar hukumar Babura.
A cewarsa mutanen da suka kubutar din sun hada da yan shekaru 16 da 27, inda suka kama su a ranar 5 ga watan Mayu a kan hanyar su ta zuwa birnin Tripoli na kasar Libya.
Haka kuma ya ce 1 daga cikin su dan Lagos ne, 2 yan Ogun ne, 1 dan Kwara ne 2 kuma daga Imo da kuma wani guda 1 daga jihar Oyo.
Kwamandan ya ce mutane suna dauke da Fasfo din Bogi, bayan bincikar su da sukayi kuma sun gano cewa suna kokarin tafiya Libya ne.
Idan za’a iya tunawa a ranar 31 ga watan Maris kimanin Mata 3 ne hukumar ta kubutar a karamar hukumar Babura wanda ake kokarin yin safarar su zuwa Libya.