Jerin sunayen shugabannin ALGON na Jihar Jigawa

0 197

Kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa (ALGON), reshen jihar Jigawa ta zabi sabbin shugabannin da za su ja ragamar kungiyar.

Wadanda aka zaba sun hadar da shugaban karamar hukumar Dutse, Bala Usman Chamo a matsayin shugaba, sai Muhammad Adamu Mukktar shugaban karamar hukumar Kazaure a matsayin sakatare da kuma shugaban karamar hukumar Hadeijia, Bala Usman T.O a matsayin ma’aji.

Da yake jawabi, sabon shugaban kungiyar, Alhaji Bala Usman Chamo ya yi alkawarin yin aikin tukuru domin sauke nauyin da aka dora musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: