Japan tana cigaba da tsaurara matan kariya a Tokyo inda zai karbi bakuncin gasar Olympic ga kuma Korona
Kasar japan tana cigaba da tsaurara matan kariya a Tokyo babban birnin kasar, yankin dake wanda zai karbi bakuncin gasar Olympic a lokacin da ake cigaba da samun karuwar masu kamuwa da cutar corona.
An dai killace yankuna dama dake cikin birnin da kuma birnin Osaka.
Fira ministan jafan Yoshihide Suga yayi gargadin cewa yaduwar da cutar ke cigaba da yi kamar wutar daji a kasar, ya umarci yan kasar da su kalli gasar wasannin daga gidajensu.
Tun da fari ministan lafiya na kasar Norihisa Tamura ya bayyana cewa kasar na cikin tsaka mai wuya lura da yadda cutar take kara yaduwa.
Kawo yanzu dai Kasar japan ta samu galaba a yakin da take da cutar inda aka samu mutane kalilan da suka harbu da cutar a cikin watanni 4.
An rawaito cewa alkaluman wanda ke kamuwa da cutar da ake tattarawa a kowace rana yakai mutum dubu 10 a ranar talatar da ta gabata, wanda kuma sama da kashi 30 cikin mutanen mazauna babban birnin kasar ne.
Hukumar shirya gasar ta Olympics ta rawaito mutane cewa 27 da suka harbu da cutar a yau jumaa yayin gasar, abinda ya kawo jumilla mutane da suka kamu cikin watan yulin da muke ciki zuwa sama da mutane 200.
Cikin matan kariyar dai, gidajen cin abinci da guraren shan barasa dole zasu daina sayar da barasa tare da takaita lokacin hada-hada.
Yankuna 3 sannanu a kasar Japan wajen tara jama’a za’a sanya dokar kulle daga ranar 2 ga watan Agusta zuwa ranar 31 ga watan.