Jam’iyyun adawa ba zasu iya haɗa kansu don tunkarar APC a zaɓen shekarar 2027 ba – Bukola Saraki

0 78

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya bayyana shakku kan yunkurin da jam’iyyun adawa ke yi na haɗe kai guri guda domin tunkarar jam’iyya mai mulki a zaɓen shekara ta 2027.

Saraki wanda ya bayyana haka a yayi wata tattaunawa da manema labarai, ya kara da cewa ko a yanzu haka akwai akalla gwamnoni jam’iyyar PDP biyar da ke matukar nuna goyon baya ga shugaba Bola Ahmad Tinubu a kokarin su na zaton cewar yin hakan zai taimaka musu wajen cimma muradan su na siyasa.

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya kuma nisanta kan sa da jam’iyyar SDP, inda ya bayyana cewa bashi da sha’awa ko tunanin barin jam’iyyar sa ta PDP.

Kalaman na Bukola Saraki na zuwa ne a daidai lokacin da yan siyasa daga mabanbanta jam’iyyun ke duba yiyuwar yin haɗin gwiwa domin ganin sun kwace ragamar mulkin Najeriya daga hannun jam’iyyar APC.

Leave a Reply