Jam’iyyar People’s Redemption Party, PRP, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shawo kan matsalar tattalin arziki da tabarbarewar matsalolin tsaro a kasar nan.
Mukaddashin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PRP, Mista Muhammed Ishaq, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
Abin takaici ne ganin yadda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta jagoranci gwamnati ta yi amfani da zarge-zargen da ba su da tushe balle makama da fargaba a yunkurin kawar da hankalinsu daga halalcin damuwar da al’ummar Najeriya ke nunawa.
A cewarsa, maimakon a ce masu zanga-zangar a matsayin ‘yan amshin shatan ‘yan adawa, kamata ya yi gwamnati ta saurari korafe-korafensu, ta kuma yi kokarin ganin ta magance matsalar rashin jin dadi. Ishaq ya ce ta hanyar tattaunawa da hadin kai na gaske ne za a iya samar da mafita mai ɗorewa ga ƙalubalen ƙasar.