Jam’iyyar PDP tace bata yanke shawarar yankin da zata kai tikitin takarar shugaban kasa ba

0 229

Jam’iyyar PDP tace baza ta yanke shawarar yankin da zata kai tikitin takarar shugaban kasa da shugabannin jam’iyyar ba, har sai an warware wasu matsaloli.

Bayan zaman ganawar kwamitin zartarwar jam’iyyar karo na 93 wanda ya samu halartar gwamnoni da ‘yan majalisa da tsaffin ministoci da wasu shugabanni, jiya a Abuja, jam’iyyar ta kuma ce ta amince da sabbin kwamitoci 2 a shirye-shiryen babban taronta na kasa mai gabatowa.

Akalla gwamnoni 8 daga cikin 13 da aka zaba a tutar jam’iyyar tare da mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, sun halarci zaman kwamitin.

Mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa Yemi Akinwonmi ya jagoranci zaman kuma shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus, bai samu halarta ba.

A wajen taron manema labarai da aka kira bayan zaman ganawar na sirri, kakakin PDP, Kola Ologbondiyan, ya gayawa manema labarai cewa kwamitin zartarwar jam’iyyar ya amince kafa kwamitin shiyar taron kasa da kwamitin karba-karba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: