Jam’iyyar PDP ta sanar da ɗage babban taron shugabaninta na ƙasa

0 193

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a kasar nan, ta sanar da ɗage babban taron shugabaninta na ƙasa karo na 99 da ta shirya gudanarwa ranar 28 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Cikin wata sanarwa da babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu ya fitar jiya Alhamis, ya ce an ɗage taron shugabannin jam’iyyar karo na 99 ne, saboda jana’izar mai ɗakin gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Umo Eno da za’a yi.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyya, ke samun saɓani da rikice-rikice tsakanin ‘ya’yanta.

Tun bayan da wata kotu ta sanar da cire shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Iyorchia Ayu a 2023, jam’iyyar ta sanar da naɗa Ilya Damagum a matsayin shugabanta na riƙo. To sai dai shi ma Damagun ya riƙa fuskantar suka daga wasu ‘ya’yan jam’iyyar waɗanda suka riƙa kiraye-kirayen ya sauka daga muƙamin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: