Jam’iyyar PDP ta mayar da martani kan kalaman Rabi’u Kwankwaso

0 103

Jam’iyyar PDP ta mayar da martani kan kalaman da sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023 ya yi wanda ya yi iƙirarin cewa jam’iyyar PDP ba ta da wani tasiri a siyasar Najeriya, inda ya ce jam’iyyar ta mutu.

A ranar Asabar ne dai Sanata Kwankwaso yayin buɗe ofishin jam’iyyar NNPP na jihar Katsina, jagoran Kwankwasiyyar ya zargi jam’iyyar PDP da APC mai mulki da jefa kanta cikin abin da ya kira ”halaka”.

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa Debo Ologunagba ya fitar a jiya Lahadi, PDP ta bayyana Kwankwaso a matsayin “mara muhimmanci a siyasar Najeriya” tare da zargin sa da son kai. Ologunagba, ya soki kalaman Kwankwaso, inda ya nuna cewa jam’iyyar NNPP a karkashin shugabancin Kwankwaso na ƙoƙarin gina kanta ne a jiha ɗaya kacal, yayin da kuma jam’iyyar PDP har yanzu na da tasiri a faɗin jihohi 13 da ke da gagarumin wakilci a majalisar dokokin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: