Jami’yyar PDP ta kalubalanci gwamnatin jihar Jigawa bisa cire kudade ba bisa ka’ida ba

0 265

Jami’yyar PDP a jihar Jigawa da kalubalanci gwamnatin jihar bisa cire kudade daga cikin asusun kananan hukumomi ba bisa ka’ida ba, domin daukar nauyin zaben kananan hukumomi dake tafe shekara mai zuwa.

Amma shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi a jihar Jigawa da hadimin gwamnan jihar sun bayyana wannan zargi a matsayin karya da kaharu.

Shugaban jami’iyyar PDP na karamar hukumar Kazaure Mustapha Ibrahim Danshatu,ya na zargin gwamnatin Jiha da cire kudaden kananan hukumomi tare da ajiye su a asusun wasu bankuna.

Yayi kira ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa Ola Olukoyede da yayi bincike kan zargin karkatar da wannan makudan kudade da gwamnatin Jigawa keyi.

Amma shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na Jihar Jigawa Bala Usman Chamo yace wannan labari ba gaskiya bane. Shima hadimin gwamnan jihar Jigawa kan ayyukan kananan hukumomi Abdurrahman Alkassim,ya musanta wannan zargin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: