Jam’iyyar APC ta amince Ganduje ya ci gaba da jagorancinta

0 43

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kaɗa ƙuri’ar amincewa da salon jagorancin shugabanta na riƙo, Abdullahi Umar Ganduje.

A taron da jam’iyyar ta kammala yau Laraba a Abuja, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun yaba da rawar da Ganduje ya taka tun bayan naɗa shi kan muƙamin a watan Agustan 2023.

Hakan na nufin cewa tsohon gwamnan na jihar Kano zai ci gaba da jagorancin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a yi babban taronta na ƙasa, inda za a zaɓi cikakken shugaba.

A watan Agustan 2023 ne kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya tabbatar da Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na riƙo na ƙasa, bayan ajiye aikin shugaban jam’iyyar da ya gabace shi, Sanata Abdullahi Adamu.

Leave a Reply