Jam’iyar APC ta yi Allah wadai da matakin da Jam’iyar PDP ta dauka na shigar da Ita kara da kuma karan Shugaban Jam’iyar na Rikon Kwarya kuma Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni a gaban Kotu.
Cikin wata Sanarwa da Sakataren Jam’iyar na Rikon Kwarya Sanata John Akpanudoedehe, ya ce Jam’iyar PDP cike take da rudani da kuma Farfaganda.
Duk da cewa, ya ce Jam’iyar APC bazata yi magana kan karar ta da PDP tayi a gaban Kotu ba, sai dai ya bukaci PDP ta mayar da hankalinta kan rikicin da ya mamaye Jam’iyar.
Jam’iyar PDP ta bukaci wata Babbar Kotu da take Abuja ta sauke Gwamna Mai Mala Buni daga kan mukaminsa na Gwamnan Jihar Yobe.
Haka kuma PDP ta bukaci Kotun ta gayyaci Mai Mala Buni akan ya bayyana a gabanta domin ya yi mata karin bayani kan mukaman da yake rike dasu na Gwamna da kuma Shugaban Jam’iya.
Sanata John Akpan, ya ce sakarci ne mayarwa da Jam’iyar PDP jawabi kan abinda tayi na shigar da kararta a gaban Kotu.