Hukumar kwastam ta kasa ta tabbatar da rasuwar daya daga cikin jamianta mai suna Hamza Abdullahi Elenwo.
Marigayin ya rasu ne a bakin aiki a wani shingen bincike dake garin Acilafiya akan hanyar Daura zuwa Kano a nan Jihar Jigawa.
Bayanin hakan na kunshe a wata Hukumar da Kakakin Hukumar Kwastan ta ƙasa Isa Suleiman ya sanyawa hannu, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki.
Sanarwar ta ce al’amarin ya faru ne a yayin da wata mota da ake zargin an shigo da ita cikin ƙasar nan ba bisa ƙa’ida ba, ta buge shi a yayin da Direban yake kokarin gujewa kamun.
An garzaya da Elenwo zuwa Asibitin Kazaure sannan aka wuce da shi zuwa Cibiyar kula da Lafiya ta Tarayya dake Katsina, inda acan aka tabbatar da mutuwarsa.
Kwamandan rundunar shiyya ta 2 Ahmadu Shuaibu, ya tabbatar da cewa zasu iya kar kokari domin nemawa mamacin adalci, yayin yanzu haka aka kama mutum guda da hannu a zargin
Marigayin ɗan asalin Fatakwal, Jihar Ribas ne, kuma ya shiga aikin Kwastam a 2013, ya rasu ya bar matarsa da ‘ya’ya biyu.