Jami’ar Sule Lamiɗo Ta Yi Hoɓɓasa A Yaƙi Da Korona A Jigawa

0 363

Jami’ar Sule Lamido dake Kafin Hausa ta bayar da tallafin sanadaran wanke hannu dake kashe kwayoyin Cututtuka ga gwamnatin jihar Jigawa a wani yunkurin bayar da nata tallafin don dakile yaduwar cutar Korona.

Da yake mika kayan tallafin ga shugaban kwamitin karta kwana kan yaki da Korona a ranar Laraba 15 ga watan Afrilu shugaban jami’ar Farfesa Lawan Sani Taura yace an gudanar da zurzurfan bincike a tsangayar kimiyya ta jami’ar kafin samar da sinadarin mai karfin kashe cututtuka da kaso 99.9.

Ana shi bangaren da yake karbar gudummawar sinadaran wanke hannun har guda 500, Shugaban kwamitin Kwamishinan ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa Dr. Abba Umar Zakari ya yaba da kokarin jami’ar na kirkirar wannan sinadari, inda ya roki jami’ar da ta kara matsa kaimi wurin binciken wasu sinadaran na yaki da cutar don gamawa da ita baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: