Jami’an tsaro sun ceto wasu matafiya 15 da ‘yan fashin daji suka sace a karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna

0 245

Dakarun operation safe haven a jiya sun ceto wasu matafiya 15 da ‘yan fashin daji suka sace a kauyen Jagindi, dake karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, yace an sace mutane 15 daga cikin motaci 2 a yankin yayin da suke tafiya.

Samuel Aruwan yace sojoji sun mayar da martani bayan kiran daukin gaggawa, inda suka tura dakaru zuwa wajen.

A cewar Samuel Aruwan, mai rike da kujerar gwamnan Kaduna, Hadiza Balarabe, ta godewa sojojin bisa daukin gaggawar da suka kai, wanda ya haifar da ceto matafiyan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: