Jami’an hukumar NDLEA sun kama tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5,344.1

0 335

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun kama wani nau’in tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5,344.1 da aka shigo da su a yankin Lekki na jihar Legas.

Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan yau a Abuja.

Hakazalika, Femi yace jami’an hukumar a ranar Talata 20 ga wata a lokacin da suke aiki sun samu bayanan sirri cewa wani kwale-kwale na dauke da kilogiram 2,910 na tabar wiwi da aka shigo da su a kusa da gabar tekun Alfa wanda ya taso daga Ghana.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan Ghana biyu Monday Saba mai shekaru 30 da Hakeem Kwana mai shekaru 27 da aka same su da kayan an kama su ba tare da bata lokaci ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: