Jami’an hukumar EFCC, mai yaƙi da cin hanci da Rashawa a Najeriya sun gayyaci tsohuwar ministar matan ƙasar, Uju Kennedy-Ohanenye domin amsa tambayoyi.
Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ce hukumar na zargin Ms Kennedy da karkatar da naira miliyan 138.4 cikin kuɗin da aka ware wa ma’aikatar a kasafin kuɗin 2023, da ɓarnatar da kuɗi da kuma saɓa ƙa’ida wajen wasu abubuwa.
Hukumar na zargin tsohuwar ministar da karkatar da kuɗin domin amfanin kanta, ciki har da kuɗaɗen da aka ware domin shirin tallafa wa mata na P-BAT.
Tsohuwar ministan ta isa harabar hukumar da safiyar ranar Alhamis, domin amsa tambayoyi, kuma bayanai na cewa har yanzu ana ci gaba da yi mata tambayoyin, kamar yadda kafofin ya da labaran ƙasar suka ruwaito.
Uju Kennedy-Ohanenye na ɗaya daga cikin ministoci biyar da Shugaban Ƙasar, Bola Tinubu ya sallama daga aiki a watan Oktoban 2024.
A watan Agustan 2023 ne shugaban ya naɗa ta a matsayin ministar kula da al’amuran matan ƙasar, matayin da ta riƙe na tsawon wata 15.