JAMB ta zargi wasu jami’o’i da bai wa dalibai guraben karatu ba bisa ka’ida ba.

0 232

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta zargi wasu jami’o’i da bai wa ‘yan dalibai guraben karatu ba bisa ka’ida ba.

JAMB ta ambaci jami’ar Abuja, wacce ta ce, an bayar da rahoton cewa tana bayar da guraben karatu ga dalibai ba tare da salahewar JAMB ba.

Hukumar ta shawarci dukkan dalibai da kar su amince da duk gurbin karatu da aka basu ba bisa ka’ida ba.

Sako da aka aika zuwa ga Mataimakin Shugaban Jami’ar Abuja, Farfesa Abdul-Rasheed Na’allah; da mai magana da yawun jami’ar, don mayar da martani, basu ce uffan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kazalika, wata sanarwa da Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na hukumar ta JAMB, Dakta Fabian Benjamin ya fitar, ta ce duk gurbin karatun da aka bayar da bisa ka’ida ba, bai halatta ba, kuma babu ruwan JAMB da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: