Jagoran darikar Shi’a a Najeriya ya zargi gwamnatin tarayya da muzguna masa tare da matarsa Zeenat

0 224

Jagoran darikar Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya zargi gwamnatin tarayya da muzguna masa tare da matarsa Zeenat, ta hanyar rike musu fasfunansu, watanni 3 bayan babbar kotun jihar Kaduna ta wanke su daga dukkan laifi.

Malamin da matarsa, wadanda ke jagorantar kungiyar ‘yan’uwa musulmi ta Shi’ah a kasarnan, an hana su samun wasu sabbin fasfunan da zai basu damar tafiya kasashen waje domin neman magani, bayan jami’an tsaro sun bayar da labarin cewa sun rasa takardunsu na tafiye-tafiye a cikin shekarun shidan da suke tsare.

Sheikh El-Zakzaky, wanda ya sanar da haka yayin wata fira da aka yi da shi a Gidan talabijin na Press TV, ya kuma zargi gwamnatin tarayya da rashin bayar da dalilin aikata hakan.

El-Zakzaky yace basu da niyyar tserewa daga kasarnan, kasancewar kotun ta wanke su kuma ta ayyanasu a matsayin marasa laifi a tuhume-tuhume guda 8 da ake zarginsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: