INEC Tace Atiku Bai Cika Ka’idojin Lashe Zaben 2023 Ba
Hukumar zaɓe Mai Zaman Kanta ta kasa INEC ta ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya gaza cika sharuɗan da kundi tsarin mulkin ƙasar ya gindaya kafin a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.
INEC ta bayyana haka ne a matsayin martani kan ƙorafe-ƙorafen da ɗan takarar ya shigar gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe.
Inda ta buƙaci kotun da ta yi watsi da ƙorafin da ɗan takarar ya shigar gabanta yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC nasara.
Hukumar ta ce Atiku ya gaza samun kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a aƙalla kashi biyu bisa uku na jihohin ƙasar 36 da kuma birnin tarayya Abuja, wanda hakan na daga cikin sharuɗan cin zaɓe a ƙasar.
Game da ƙorafin saɓa dokar zaɓe, INEC ta ce an gudanar da zaɓen ne bisa dokar zaɓen ƙasar ta 2022, ba tare da almundahana ba, kamar yadda masu ƙorafin suke zargi.
Hukumar zaɓen ta sake jaddada cewa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC shi ne halastaccen zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.
Game da ƙorafin rashin samun rinjayen ƙuri’u a birnin Tarayya Abuja da ake yi kan Tinubu, INEC ta ce kundin tsarin mulkin ƙasar bai ware wani matsayi na musamman kan ƙuri’un birnin Abuja ba
A cewarta ƙuri’un birnin Abuja daidai suke da ƙuri’un kowacce jiha ta fuskar matsayi.