INEC ta tabbatar da yadda ta kammala shirin zaben gwamna a jihar Edo

0 182

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta tabbatar da yadda ta kammala shirin zaben gwamna a jihar Edo da za’a fafata tsakanin jam’iyyu gobe asabar.

Wannan na zuwa yayin da aka samu zazzafar adawa tsakanin yan takara dake son lashe zaben na gobe.

Jamiyyun siyasa 17 ne za su fafata a wannan zabe to sai dai jamiyyu 3 na APC  da PDP da LP ne hankula ya karkata kansu.

Sanata Monday Okpebholo ne ke wa jamiyyar APC takara ita kuwa PDP ta tsayar da Asue Ighodalo a matsayin dan takararta, Olumide Akpata na jam’iyyar Labour.

Hajiya Zainab Aminu Abubakar mai magana da yawun hukumar INEC ta kasa ta tabbatarwa manema labarai cewa tuni suka aike da kaya zuwa ƙananan hukumomin jihar Edo baki ɗaya kuam suna jiran gobe ne asabar don gudanar da zabe.

Haj. Zainab Aminu ta bada tabbacin cewar hukumar zaben ƙasar INEC za ta yi zabe na adalci tare da miƙa nasara ga wanda alumma suka zabe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: