INEC ta kaddamar da shafin internet domin wadanda suka isa zabe su yi rijista
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kaddamar da shafin internet domin wadanda suka isa zabe su yi rijista.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kaddamar da shafin, shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu, yace an samar da shafin domin wadanda ke bukatar yin rijista su fara rijistar ta internet.
Ya bukaci wadanda ke so suyi zabe da suyi rijista ta hanyar bayar da bayanan da ake bukata kafin ya nemi zuwa ofishin hukumar domin karasa rijistar.
Mahmud Yakubu yace a saboda kalubalen tsaro a wasu sassan kasarnan, hukumar ta yanke shawarar fara rijistar ta internet kafin ta kaddamar da farawa gabadaya a dukkan cibiyoyin rijistar guda dubu 2 da 673 dake fadin kasarnan.
Hukumar ta dakatar da aikin rijistar watanni shida kafin zaben gama gari na shekarar 2019.