INEC ta ce nan ba da dadewa ba za ta dauki mataki kan dakatarwar da aka yi wa Hudu Ari

0 316

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce nan ba da dadewa ba za ta dauki mataki kan dakatarwar da aka yi wa kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Hudu Ari.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na kasa INEC, Festus Okoye ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai jiya a Abuja.

Idan zamu iya tunawa dai Hudu Ari ya jawo cece-kuce a lokacin da ya bayyana sakamakon zaben gwamna a jihar Adamawa, tun kafin ma a kammala tattara sakamakon zaben jihar.

Inda ya bayyana Sanata Aisha Dahiru Binnani a matsayin wacce ta lashe zaben ba bisa ka’ida ba.

Bayan faruwar lamarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a binciki duk wani jami’an tsaro da ke da hannu a wannan aika-aikar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: