Malam Ibrahim Yahaya Sidi Na Khalifa, mahaifin amaryar da aka kashe a Talatar da ta gabata kwanaki 54 kacal da daura mata aure, ya nemi a bi masa hakkin ’yarsa da aka kashe.
Amina Aliyu, ita ce matar da ake zargin yi wa kishiyarta kisan gilla a unguwa Tunga da ke Jihar Neja.
A wata tattauna ta musamman tare da Aminiya, Malam Na Khalifa ya ce yana fatan shari’a za ta yi aiki ta hanyar tabbatar da cewa an hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
A cewarsa, Musulunci ya yarda cewa babu laifi ga wanda aka zalunta kuma yanke shawarar a bi masa hakki inda ya buga hujja da yadda Alkur’ani mai girma ya yi bayani hukuncin wanda ya kashe wani ba tare da wani dalili na adalci ba.
“Ba zan taba yafe jinin ’ya ta ba don Alkur’ani ya ce babu wata rai da ta fi wata, kuma duk wanda ya kashe a kashe shi, saboda haka ina son ganin a zartar da hukunci a kan wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.”
“A’a sam ba zan taba yafe musu ba, idan hatsari ne ko kisan kai ba da gangan ba, to wannan wani batu ne na daban.
“Amma a yi wa diya ta dukan da ya yi ajalinta, kuma ba a tsaya iyaka nan ba, sai da aka cinna wa gawarta wuta, wannan wani abu da ba zan taba yafewa ba,” a cewar mahaifin cikin zubar hawaye.
Malam Na Khalifa, ya ce labarin mutuwar ’yarsa ya zo masa da farin ciki da kuma bakin ciki a lokaci guda.
A cewarsa, farin cikin ya samo asali ne daga yakini a kan furucin Annabi Muhammmad (SAW), wanda ba ya fadin komai sai gaskiya, domin kuwa ya yi bushara da duk wanda aka kashe bisa zalunci zai dawwama a Aljanna.
“Dangane da waccan busharar, ba ni da shakkar a kan cewa ’yata za ta kasance cikin ’yan Aljanna kuma hakan a faranta min rai.”
“Sai dai kuma, na yi bakin ciki da matukar damuwa kasancewar ba zan kara ganinta ba a wannan duniyar kuma ina cikin bakin cikin tunanin abin da ta fuskanta a hannun wadanda suka kashe ta,” in ji shi.
Mahaifin ya misalta ’yarsa a matsayi mutuniyar kirki mai son zaman lafiya da kuma kyawawan dabi’u, wanda a cewarsa ta sha bamban da sauran ’yan uwanta ta fuskar kyawun halayya.
Ya ce duk da cewa ba shi da kudin da zai iya daukaka karar, amma ya yi murna da jin cewa Sarkin Minna ya sa hannu a lamarin kuma wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun suna sha’awarsu domin ci gaba da ganin adalci ya tabbata har zuwa karshen lamarin.