Ina sane da irin sadaukarwar da ‘yan Najeriya ke yi game da sauye-sauyen da gwamnatina ke aiwatarwa

0 255

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce yana sane da irin sadaukarwar da ‘yan Najeriya ke yi game da sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa, tun bayan hawansa mulki a watan Mayun wannan shekara.

Haka nan, ya bayyana 2023 a matsayin shekarar sauyi a Najeriya yana mai cewa sauye-sauyen da ake aiwatarwa sun zama tilas don samun kasa mai yalwar arziki.

A cewar mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Mr. Bayo Onanuga yace shugaban Kasar  zai cigaba da daukar matakan bunkasa Najeriya a 2024.

Yace shugaban Kasar  bai taba yarda da matakan wucin gadi wajen gyara fasalin kasar ba.

Onanuga ya lura cewa, cire tallafin man fetur da kuma yunkurin dai-daita farashin canjin kudaden waje, da gwamnatin Tinubu ta bullo da su tun a karshen watan Mayu, sun haifar da matsalolin tsadar man fetur da faduwar darajar Naira. Ya ce sabon rahoton da hakumar kiddiga ta kasa NBS ta fitar ya nuna hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai kashi 26.7 cikin 100 a watan Satumba, wanda ya tashi zuwa kashi 28.2 a watan Nuwamba daga kashi 27.33 cikin 100 a watan Oktoba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: