
Ƙungiyoyin farar-hula da rajin yaƙi da cin hanci da rashawa sun ce ya kamata mahukunta a ƙasar su dinga yin bayani dalla-dalla a kan kadarori da kuma kuɗaɗen da suke ƙwata daga hannun ɓarayin gwamnati ta yadda ƴan ƙasa za su fahimci abin da ake yi.
Ƙungiyar CISLAC mai sa ido a kan harkokin majalisun dokoki ta ce akwai bukatar a kafa doka da za ta ba da damar baje-kolin irin wadannan kadarorin, tana zargin cewa ana nuku-nuku a yadda ake tafiyar da lamarin.